Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, Ya ƙaddamar da wani Sabon Shiri na Taimakon Jin Kai, da nufin tallafawa Mutane kusan Miliyan 1.8 masu buƙata. Rabon da aka ƙaddamar a Sansanin Ƴan Gudun hijira na Muna dake ƙaramar Hukumar Jere, Ya Shafi Gidaje 300,000, Tare da matsakaicin Mutum shida A Kowane Gida.
Gwamnan ya jaddada Cewa Jihar Borno ta fara rabon Kayan abinci na farko Kimanin wata ɗaya da ya Gabata, Wanda yayi dai-dai da Sanarwar Gaggawar Abinci da Fadar Shugaban ƙasa ta fitar. Da yake Amsa kiran da Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu yayi na magance matsalar abinci, Gwamnatin Zulum ta tsawaita Shirin bayar da Tallafin, Inda ta bayar da tsabar kuɗi Naira 5,000, buhun shinkafa, buhun wake, Ga duk wanda ya Cancanta.
Bugu da ƙari, Gwamna Zulum ya Rabawa Gidaje 400 Ga Marasa Galihu Daga kauyuka biyar da mayakan Boko Haram suka raba da Gidajensu a Molai. Tallafin Ya haɗa da shinkafa, Hatsi Masara, tabarmi, haɗe, Da Tallafin kuɗi.
CNN Hausa Nigeria

Comments
Post a Comment