Gombe
Halilu Mohammed Teli
Wasu manyan masu ruwa da tsaki daga Jihar Gombe sun bayyana goyon bayansu ga takarar Dr. Jamil Isyaku Gwamna na gwamnan jihar a zaɓen 2027 ƙarƙashin jam'iyyar APC.
A cikin wata sanarwar manema labarai da mai magana da yawun Dr. Gwamna, Ibrahim Sani Shawai, ya fitar, an ce an cimma wannan matsaya ne a taron tattaunawar masu ruwa da tsaki na Jihar Gombe da aka gudanar a Abuja, ƙarƙashin jagorancin Mai Bai wa Mataimakin Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Musamman, Dakta Aliyu Modibbo Umar.
Sanarwar ta ce taron ya samu halartar tsofaffin ministoci huɗu, manyan hafsoshin soja masu ritaya huɗu, tsohon Air Vice Marshal guda ɗaya, tsofaffin sakatarorin gwamnati, jakadu masu ritaya, furofesoshi, ƙwararrun ma'aikatan gwamnati, 'yan kasuwa da kuma matasa ƙwararru daga Jihar Gombe.
Bayan tattaunawa kan makomar siyasar jihar da shirye-shiryen zaɓen 2027, mahalarta taron sun amince da wasu shawarwari da suka haɗa da ƙarfafa haɗin kan jam'iyya, faɗaɗa wayar da kan jama'a a matakin ƙasa da kuma ƙarfafa goyon baya ga jam'iyyar APC.
Daya daga cikin manyan matsayoyin da aka cimma shi ne amincewa baki ɗaya da Dr. Jamil Isyaku Gwamna a matsayin wanda suke goyon baya ya tsaya takarar gwamnan Jihar Gombe a 2027. Sun ce sun yanke wannan hukunci ne bisa abin da suka bayyana a matsayin ƙwarewarsa ta shugabanci, hangen nesa da kuma ƙudirin ci gaban jihar.
Har ila yau, taron ya jaddada cewa dandalin masu ruwa da tsakin na Jihar Gombe zai ci gaba da kasancewa ƙungiyar tuntuba da za ta tallafa wa jam'iyyar APC da gwamnatin jihar da sauran masu ruwa da tsaki, ba tare da kafa wata sabuwar tsarin siyasa ba.
Maharta taron sun kuma amince da kafa sassan siyasa da na fasaha domin kula da hulɗa da masu ruwa da tsaki, tsara manufofi, gudanar da bincike, wayar da kan jama'a da kuma yaɗa bayanai.
Haka kuma an kafa wani kwamitin sulhu da hulɗa da masu ruwa da tsaki domin tattaunawa da tsofaffin masu neman takara da magoya bayansu, da nufin ƙarfafa haɗin kai a cikin jam'iyyar kafin zaɓen 2027.
Sanarwar ta ƙara da cewa taron ya yi kira da a ƙara zage dantse wajen wayar da kan al'umma a dukkan ƙananan hukumomi, gundumomi da rumfunan zaɓe, tare da ƙarfafa rajistar masu kaɗa ƙuri'a da kuma siyasar da ta ginu kan ƙwarewa, gaskiya da haɗa kan kowa.
Da yake jawabi bayan samun wannan goyon baya, Dr. Jamil Isyaku Gwamna ya ce amincewar da aka nuna masa za ta ƙara masa ƙwarin gwiwar ci gaba da mayar da hankali kan hidimar al'umma da bunƙasa ci gaba domin ya kai ga kowane yanki da kowane ɗan jihar.
:::
Comments
Post a Comment