Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya CON, ya samu labarin rasuwar Shugaban Jam'iyyar APC na Karamar Hukumar Akko, Alhaji Usman Waziri Jabbo cikin kaɗuwa da jimami.
Alhaji Usman Waziri Jabbo ya rasu ne jiya Alhamis bayan gajeruwar rashin lafiya.
Gwamnan ya bayyana marigayi jigon na Jam’iyyar APC a matsayin jagora mai mutunci, jajirtaccen ɗan siyasa tun daga tushe wadda ya yi wa al’umma da jiharsa hidima sosai.
Yace rasuwar Shugaban Jam’iyyar ta APC na Akko babban rashi ne, ba ga iyalansa da magoya bayan jam’iyyar kaɗai ba, har ma da Jihar Gombe baki ɗaya.
Gwamna Inuwa yace “Duk wanda ya san Alhaji Jabbo zai riƙa tunawa tare da girmama shi saboda kwazo da hidimar da ya yi wa jam’iyyar, da al’ummar yankinsa dama jiharsa, kasancewar gudumawar da ya bayar ga jam’iyyar APC da gwamnati mai ci ya bar gurbin da ba za a taɓa mantawa da shi ba. kuma za a yi kewar rashinsa matuƙa.
Gwamnan a madadin gwamnati da al’ummar Jihar Gombe, ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, da jam’iyyar APC, dama ɗokacin al’ummar Ƙaramar Hukumar Akko, yana mai addu’ar Allah ya jiƙansa yasa Aljannar Firdausi ce makomarsa, ya baiwa waɗanda ya bari haƙurin jure wannan babban rashi.
Ismaila Uba Misilli
Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Gombe

Comments
Post a Comment