Skip to main content

Uwargidan Gwamnan Jihar Gombe, Hajiya Dr. Asma’u Inuwa Yahaya Ta Kaddamar Da Yakin Neman Shigar Da ‘Ya’yan Da Ba Su Shiga Makaranta Ba





Uwargidan Gwamnan Jihar Gombe, Hajiya Dr. Asma’u Inuwa Yahaya, ta kaddamar da yakin wayar da kai domin rage yawan ‘ya’yan da ba sa zuwa makaranta tare da fadada damar samun ingantacciyar ilimi a fadin jihar.

A lokacin bikin kaddamarwar da aka gudanar a Gombe, Uwargidan Gwamnan ta bayyana ilimi a matsayin mafi inganci wajen karya tarkon talauci da kuma gina al’umma mai albarka da ci gaba.

A cewarta: “Babu wani yaro da ya kamata a bar shi a baya. Ilimi ba kawai hakki ba ne, shi ne gindin kafa damar samun makoma mai haske ga ‘ya’yanmu, al’ummarmu da kuma jiharmu mai daraja.”

A cikin shirin, Gwamnatin Jihar Gombe ta bada tabbacin bayar da tallafin kudi ga makarantun firamare 50 da za su yi kokarin dawo da yaran da suka bar makaranta. Wannan, kamar yadda ta bayyana, zai zama karin karfafa gwiwa ga makarantu da al’umma domin baiwa ilimi mai shigar kowa muhimmanci.

Shugaban Hukumar Ilimi Bai Daya  ta Jihar Gombe (SUBEB), Alhaji Babaji Babadidi, ya yaba wa Uwargidan Gwamna bisa jajircewarta wajen jagorantar wannan yunkuri na ilimi. Ya tabbatar da cewa SUBEB zai kara azama wajen wayar da kan al’umma, shiga zukatan jama’a da kuma fadakar da iyaye domin tabbatar da cewa kowane yaro ya samu damar karatu.

A cewarsa: *“Wannan yaki na zuwa a kan gaba domin taimaka mana mu kai ga yara mafiya rauni. SUBEB zai  hada hannu da iyaye, al’umma da abokan cigaba domin tabbatar da cewa idan yara sun shiga makaranta, za su ci gaba da zama har su kammala karatunsu.”

Haka zalika, Shugaban shirin (UBEC) ya jinjinawa wannan shiri, inda ya bayyana cewa ya yi daidai da kokarin Gwamnatin Tarayya na rage yawan yaran da ke zaune a gida ba tare da shiga makaranta ba.

A nata jawabin, Kwamishinan Ilimi ta Jihar Gombe, Dr. Aishatu Maigari, ta sha alwashin cewa ma’aikatarta za ta bayar da cikakken goyon baya ga shirin, tana mai jaddada cewa ilimi shi ne ginshikin cigaban dan Adam a jihar. 

Shima, Shugaban Karamar Hukumar Gombe,Barr Sani A.A.Aliyu ya sake tabbatar da shirin hukumar wajen gudanar da wayar da kai a matakin al’umma domin tabbatar da cewa iyaye sun rungumi wannan yunkuri na shigar da ‘ya’ya makaranta.

Babban abin da ya kayatar a wajen taron shi ne yin rajistar yara ta alama da Uwargidan Gwamna tare da sauran manyan baki, wanda hakan ya nuna kaddamar da shirin a hukumance a fadin Jihar Gombe.

Uwargidan Gwamna ta sake jaddada kudirinta na ci gaba da jagorantar yunkurin tabbatar da cewa ilimi ya zama kayan karfafawa, cigaba da kuma sauyi mai dorewa ga rayuwar ‘ya’yan Jihar Gombe.

Zahrah Umar Adamu
Babbar Mai Taimakawa ga Gwamnan Jihar Gombe,
Ofishin Uwargidan Gwamna.




Comments

Popular posts from this blog

Football Unites Gombe South as All Stars FC Win Unity Cup

All Stars FC of Kaltungo have emerged champions of the 9th edition of the Adamu Yola Gombe South Unity Cup, following a dramatic 3–2 penalty shootout victory over Oska FC after regulation time ended 1–1. The thrilling final, played at the Olusegun Obasanjo Stadium, saw Oska FC take the lead in the first half.  However, All Stars FC drew level from the penalty spot after Oska’s goalkeeper committed an infringement inside the box. Despite dominating the second half and creating several clear scoring chances, Oska FC failed to convert, a miss that would later prove costly.  Oska FC lost both their first and second goalkeepers after receiving red cards in the previous match. an outfield player step in as makeshift goalkeeper and produced two brilliant saves during the shootout, three Oska players missed their spot kicks, handing All Stars FC the title. Earlier in the third-place match, Dinge Flying Bees defeated Chonge FC 3–0 on penalties after a goalless draw to claim...

Kolmani Oil Discovery Spurs Academic Expansion at GSU

The Vice Chancellor of Gombe State University, Prof. Sani Ahmed Yauta, has reaffirmed his commitment to elevating the institution to international prominence through academic excellence, research innovation, and strategic partnerships. Addressing newsmen in his office, Prof. Yauta expressed profound appreciation to Governor Muhammadu Inuwa Yahaya for confirming his appointment, describing the governor’s support for the university as “immeasurable and unprecedented.”  He assured that he would work tirelessly to justify the confidence reposed in him by the state government. The Vice Chancellor disclosed that the university is developing new academic programmes in petroleum, gas, and energy-related studies to strategically align with opportunities arising from the Kolmani oil exploration.  According to him, the discovery of oil and gas in the Kolmani axis presents a unique opportunity for Gombe State University to play a key role in training skilled manpower for the e...

Unity in Action: Defending Champions,Binge Flying Bees vs Super Lions to Light Up Adamu Yola Cup 2025 Opener

By Halilu Mohammed Teli  Football fever is set to grip Gombe South once again as the 9th edition of the Adamu Yola Gombe South Unity Cup officially kicks off, with Binge Flying Bees taking on Super Lions Kalshin in what promises to be a thrilling opening encounter on the 5th of December 2025, at Olusegun Obasanjo Stadium, Kaltugo. This year’s draws, conducted at Amdo Adore Event Center, Kaltugo,Kaltungo Local Government Area, brought together a record 64 football clubs drawn from across Kaltungo, Billiri, Balanga, and Shongom LGAs. The massive turnout underlines the competition’s reputation as the biggest grassroots football tournament in Gombe State and one of the most consistent community-driven competitions in Nigeria. The clubs were grouped into different centres: Kaltungo Centre: 37 clubs, grouped into Pools A–I Billiri Centre: 18 clubs, grouped into Pools A–E Shongom Centre: 9 clubs, grouped into Pools A–B This wide participation highlights the growing interest of...